83 da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.
Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.