28 ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon.
Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.