23 da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuwar.
Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji.