Sa’an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa wajen mutane ya sa musu albarka. Da yake ya miƙa hadaya don zunubi, hadaya ta ƙonawa da kuma hadaya ta salama, sai ya sauka.
“ ‘Wannan ita ce dokar Banazare wanda ya yi alkawari ga Ubangiji bisa ga keɓewarsa, tare da duk abin da zai iya bayarwa. Tilas yă cika alkawarin da ya yi bisa ga dokar zaman Banazare.’ ”
Firistoci, ’ya’yan Lawi maza, za su fito, gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su su yi masa hidima, su kuma furta albarku a cikin sunan Ubangiji, za su kuma daidaita duk rigimar cin mutunci.