Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 4:19 - Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Saboda su rayu, kada su mutu sa’ad da suka zo kusa da abubuwa mafi tsarki, a yi musu wannan, wato, Haruna da ’ya’yansa za su shiga wuri mai tsarki su ba wa kowane mutum aikinsa da kuma abin da zai ɗauka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

19 ta hallaka ta wurin kusatar waɗannan tsarkakakkun abubuwa. Maganin abin, shi ne sai Haruna da 'ya'yansa maza, su shiga, su nuna wa kowannensu irin aikin da zai yi, da kayan da zai ɗauka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 4:19
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Bayan Haruna da ’ya’yansa suka gama rufe kayayyaki masu tsarki da dukan abubuwa masu tsarki, sa’ad da kuma aka shirya tashi daga sansani, sai Kohatawa su zo gaba, su ɗauka. Amma kada su taɓa abubuwa masu tsarki, don kada su mutu. Kohatawa za su ɗauki abubuwan da suke cikin Tentin Sujada.


Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.


“Ku tabbata cewa ba a kawar da zuriyar Kohatawa daga Lawiyawa ba.


Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.


sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu.


Za su kasance a ƙarƙashinka, su ne kuma za su yi dukan hidima ta Tenti, amma kada su je kusa da kayayyakin wuri mai tsarki, ko bagade, in ba haka ba, da kai da su, za ku mutu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ