“Za a kawo dukan matanka da ’ya’yanka wa Babiloniyawa. Kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba amma za su sa sarkin Babilon zai kama ka; za a kuma ƙone wannan birni.”
Amma Allah ya kashe waɗansu mutum saba’in na mutanen Bet-Shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawarin Ubangiji. Mutane kuwa suka yi makoki domin Ubangiji ya hallaka mutane da yawa.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”
sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu.
Saboda su rayu, kada su mutu sa’ad da suka zo kusa da abubuwa mafi tsarki, a yi musu wannan, wato, Haruna da ’ya’yansa za su shiga wuri mai tsarki su ba wa kowane mutum aikinsa da kuma abin da zai ɗauka.