Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ƙidaya 35:30 - Sabon Rai Don Kowa 2020

30 “ ‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

30 Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ƙidaya 35:30
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku.


Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’


Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.


Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”


Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku.


Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.”


“Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”


“ ‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan.


“Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi.


“ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.


“ ‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi.


“La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ