Ƙidaya 30:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Amma in mijin ya warware su sa’ad da ya ji, to, ba wani alkawari ko rantsuwar da ya fito daga leɓunanta da zai tabbata. Mijinta ya warware su, Ubangiji kuma zai gafarce ta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Amma idan mijinta ya hana ta a ranar da ya ji, to, sai ta bari. Mijinta ya hana ta ɗaukar wa'adin, Ubangiji kuwa zai gafarce ta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.