23 Ku shirya wannan tare da hadaya ta ƙonawa ta kowace safiya.
23 Za a miƙa waɗannan hadayu banda hadaya ta ƙonawa wadda akan miƙa kowace safiya.
Ka gaya musu, ‘Ga hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, da za ku miƙa wa Ubangiji, raguna biyu, bana ɗaya-ɗaya, marasa lahani.
Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace Asabbaci, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da ta hadaya ta sha.
Ta haka za a shirya abinci don hadayar da aka yi da wuta, kowace rana, har kwana bakwai don daɗin ƙanshi ga Ubangiji; a shirya shi haɗe da hadaya ta ƙonawa ta kullum, da kuma hadaya ta sha.