(Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist.
Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su.