Ƙidaya 23:24 - Sabon Rai Don Kowa 202024 Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya; sun tā da kansu kamar zaki wanda ba ya hutawa sai ya cinye naman abin da ya kama ya kuma sha jinin abin da ya kama.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki24 Ga shi, jama'ar Isra'ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki, Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa. Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.