‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?
A wannan dare, Allah ya zo wurin Bala’am ya ce, “Da yake waɗannan mutane sun zo su tafi da kai, to, ka tafi tare da su, sai dai ka yi abin da na ce ka yi ne kaɗai.”
Sa’an nan Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su; a nan kana ganin sashe ne kawai, ba dukansu ba. Daga can kuwa, ka la’anta mini su.”
Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.