Ƙidaya 20:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 amma da muka yi kuka a gaban Ubangiji, ya kuwa ji mu, sai ya aiko mala’ika, ya fitar da mu daga Masar. “Yanzu ga mu a Kadesh, garin da yake kan iyakar yankinka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?