A maimako haka, na ba wa Lawiyawa zakka da Isra’ilawa suka kawo domin hadaya ga Ubangiji, a matsayin gādonsu. Shi ya sa na ce game da su, ‘Ba su da gādo a cikin Isra’ilawa.’ ”
“Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji.