Ƙidaya 18:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma.