Waɗannan su ne kayayyakin da aka yi amfani da su domin aikin tabanakul, da tabanakul na Shaida, waɗanda aka rubuta bisa ga umarnin Musa ta wurin Lawiyawa, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.
A maimakon haka sai ka naɗa Lawiyawa su lura da tabanakul Shaida, wato, kan dukan kayayyaki da kuma kome da yake na wuri mai tsarki. Za su ɗauko tabanakul da dukan kayayyakinsa; za su lura da shi, su kasance kewaye da shi.
Amma Lawiyawa za su kafa sansaninsu kewaye da tabanakul na Shaida. Don kada fushi yă fāɗo a kan al’ummar Isra’ilawa. Hakkin Lawiyawa ne su kula da tabanakul na Shaida.”
Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.