Ƙidaya 15:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki29 Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.