Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.”
Ubangiji zai komar da ku cikin jiragen ruwa zuwa Masar, tafiyar da na ce kada ku ƙara yi. A can za ku ba da kanku don sayarwa ga abokan gābanku a matsayin bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku.
amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?” ’ ”