Ƙidaya 14:33 - Sabon Rai Don Kowa 202033 ’Ya’yanku za su zama makiyaya a nan, shekaru arba’in suna shan wahala domin rashin amincinku, har sai mutum na ƙarshe a cikinku ya kwanta a hamada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki33 'Ya'yanku za su yi yawo a jeji shekara arba'in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.