Shi ne zai gina haikalin Ubangiji, za a kuma martaba shi da daraja, zai kuma zauna yă yi mulki a kan kursiyinsa. Zai zama firist a kan kursiyinsa. Kuma a tsakanin biyun za a sami zaman lafiya.’
Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama.