Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.
Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka.
Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim.
tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,
Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.