45 Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu.
Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa.
Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.
A cikin wannan hamadan, jikunanku za su fāɗi, kowanne a cikinku mai shekara ashirin ko fiye, wanda aka ƙirga shi cikin ƙidaya, wanda kuma ya yi gunaguni a kaina, da zai shiga wannan ƙasa.