38 Daga zuriyar Dan. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Yaron Dan shi ne, Hushim.
Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne.
Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne.
A arewa za a sami sashen sansanin Dan, a ƙarƙashin ƙa’idarsu. Shugabansu shi ne Ahiyezer ɗan Ammishaddai.