32 Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”
Mutane daga Negeb za su mamaye duwatsun Isuwa, mutane kuma daga gindin tuddai za su mallaki ƙasar Filistiyawa. Za su mamaye filayen Efraim da Samariya, Benyamin kuwa zai mallaki Gileyad.