9 Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
9 Za ta zamar maka rawanin daraja.”
Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.
A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki zai zama rawani mai daraja kyakkyawan rawani wa mutanensa da suka ragu.
Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.
Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka.
Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.
Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna.
Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani.