Saboda ka harzuƙa gāba da ni kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma ta hanyar da ka zo.
Dukan mutanen duniya ba a bakin kome suke ba. Yakan yi abin da ya gamshe shi da ikokin sama da kuma na mutanen duniya. Babu mai hana shi ko yă ce masa; “Me ka yi?”
Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.