“Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji.
Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu.