Ishaya 55:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Za ku fita da farin ciki a kuma bi da ku da salama; duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa a gabanku, dukan itatuwan jeji kuma za su tafa hannuwansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 “Za ku fita daga cikin Babila da murna, Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama. Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa, Itatuwa za su yi ta sowa don murna! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.