A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.
Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan?
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama ta hannunsa kuma mai iko cewa, “Ba zan ƙara ba da hatsinki ya zama abinci ga abokan gābanki ba, baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin wanda kika sha wahala samu ba;