Ishaya 51:13 - Sabon Rai Don Kowa 202013 har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki13 Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku, Wanda ya shimfiɗa sammai, Ya kuma kafa harsashin ginin duniya? Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku, Da waɗanda suke shiri su hallaka ku? Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi.