Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika.
Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’
Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.