Ishaya 5:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun, Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau. Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu, Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin. Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna, Amma ko wannensu tsami take gare shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana.