Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.
Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
“ ‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe.
Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.
Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”
a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.
Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’ ” Haruna ya yi shiru.
Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa? Bari wanda yake tafiya cikin duhu, wanda ba shi da haske, ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.