Ishaya 49:18 - Sabon Rai Don Kowa 202018 Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye; dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki. Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “Za ki yafa su duka kamar kayan ado; za ki yi ado da su, kamar amarya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki18 Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa! Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida! Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai, Za ki yi fāriya da mutanenki, Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.