Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.”
Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”
“Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”