Ishaya 48:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila, Ku da kuke zuriyar Yahuza. Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji, Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila, Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.