Ishaya 47:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 “Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya. Kin ɗauka kina da girma kamar Allah, Har kina ganin ba wani kamarki. Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba, Ko ki sha hasarar 'ya'yanki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.