Ishaya 42:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki5 Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.