Ishaya 42:13 - Sabon Rai Don Kowa 202013 Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi, kamar jarumi zai yi himma; da ihu zai tā da kirarin yaƙi zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki13 Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi, Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi. Ya yi gunzar yaƙi da tsawar yaƙi, Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.