Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 41:22 - Sabon Rai Don Kowa 2020

22 “Ka shigar da gumakanka don su faɗa mana abin da zai faru. Faɗa mana abubuwan da suka riga suka faru, domin mu lura da su mu kuma san abin da zai faru a ƙarshe. Ko kuwa ku furta mana abubuwan da za su faru,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

22 Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba, Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru, Ku faɗa mana yadda zai zama duka, Domin lokacin da ya faru mu mu sani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 41:22
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni.


“Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.


Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.


Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji. Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā, mene ne kuma bai riga ya faru ba, I, bari yă faɗa abin da zai zo.


Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku.


“Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi.


Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.”


Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani, ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’? Ba wanda ya faɗa wannan, ba wanda ya riga faɗe shi, ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.


na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni, bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su; sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.


“Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ