Ishaya 40:20 - Sabon Rai Don Kowa 202020 Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki20 Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba, Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yana neman gwanin sassaƙa Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.