Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 40:19 - Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa, maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

19 Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi, Maƙera kuma suka dalaye da zinariya, Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 40:19
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye.


Saboda haka ya mayar da azurfan wa mahaifiyarsa, ita kuwa ta ɗauki azurfa ɗari biyu na shekel ta ba wa maƙeri, wanda ya mai da su sura da kuma gunki. Aka kuwa sa su a gidan Mika.


Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya.


A wannan rana mutane za su zubar wa jaba da jamage gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya da suka yi don su bauta musu.


Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.


Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi.


Ƙasarsu ta cika da gumaka; sukan rusuna ga aikin hannuwansu, ga abin da yatsotsinsu suka yi.


Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”


Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ