Ishaya 39:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Hezekiya kuwa ya marabci manzannin, ya kuma nunnuna musu dukiyarsa, wato azurfa da zinariya, da kayan yaji da na ƙanshi, da dukan kayayyakinsa na yaƙi. Ba abin da bai nuna musu ba a ɗakunan ajiya, da ko'ina a mulkinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.