Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 38:19 - Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

19 Masu rai ne suke yabonka, Kamar yadda nake yabonka yanzu. Iyaye za su faɗa wa 'ya'yansu irin amincinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 38:19
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.


Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.


Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku.


Ku faɗa wa ’ya’yanku, bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu, ’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.


Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina.


Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.


Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.


Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.


Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”


Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.


Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.


don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”


Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ