Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”
sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo.