Ishaya 37:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Sarkin Assuriya ya aiko babban shugaban mayaƙansa don ya zagi Allah mai rai. Da ma Ubangiji Allahnka ya ji waɗannan zage-zage ya kuma hukunta waɗanda suka yi su. Don haka sai ka yi addu'a ga Allah saboda mutanenmu waɗanda suka ragu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”