Ishaya 36:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Kuma in ka ce mini, “Mun dogara ga Ubangiji Allahnmu ne” ba shi ba ne Hezekiya ya rurrushe masujadan kan tudunsa da bagadansa, yana ce wa Yahuda da Urushalima, “Dole ku yi sujada wa gaban wannan bagade”? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa'an nan ya faɗa wa jama'ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.