Ishaya 36:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin Sarki Hezekiya, Sennakerib sarkin Assuriya ya kai wa dukan birane masu kagaran Yahuda yaƙi ya kuma kame su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 A shekara ta goma sha huɗu da Hezekiya yake sarautar Yahuza, sai Sennakerib Sarkin Assuriya ya tasar wa birane masu kagara na Yahuza, ya kame su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.