Ishaya 30:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.