Ishaya 30:30 - Sabon Rai Don Kowa 202030 Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki30 Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.